Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar ta bude shafin intanet musamman domin rijistar rigakafin Korona.

Hukumar Lafiya matakin Farko ce za ta jagoranci shafin domin yi wa ƴan Najeriya rigakafin cutar.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya rak kafin karɓar rigakafin cutar a Najeriya.

Za a karɓi rigakafin cutar a gobe Talata kamar yadda shugaban kwamitin yaƙi da cutar a ƙasar Boss Mustapha ya bayyana.

Adadin rigakafin da za a karɓa na COVAX ya kai kusan miliyan huɗu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: