Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani mai suna Sada Adamu mazaunin garin Rano wanda ya kware wajen koya wa masu garkuwa da mutane harbin bindiga.

Wanda ake zargi ya bayyana cewar tun a baya ya kware wajen satar kaji, awaki da tumaki amma daga baya ya karɓi tayin satar mutane daga wani abokin sa mai suna Ibrahim.

Mutumin ya taɓa yin garkuwa da wani mutum a da motar sa a Kwana Ɗan’gora har su ka kwace kudi naira dubu ɗari huɗu sannan su ka karɓi kudin fansa miliyan ɗaya daga ƴan uwan sa.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin mai da shi sashen binciken manyan laifuka don faɗaɗa bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: