Hukumomi a Najeriya sun karɓi rigakafin cutar Korona wadda aka daɗe ana jiran zuwan ta daga ƙasar Indiya.
Rigakafin ta kai miliyan 3,924,000.
An kawo rigakafin ne daga ƙasar Indiya a jirgin Emirate wanda ya sauka afilin sauka da tashin jiragen sama na babban binin kasar wato Abuja.
Hukumar lura da ingancin abinci a Najeriya NAFDAC da sauran masu ruwa da tsaki a harkar za su shiga bincike don tabbatar da ingancin rigakafin.
Za a yi binciken ne a gobe da jibi, kuma za a fara yin gwajin allurar rigakafin ne a kan hukumomin lafiya a ranar Juma’a.
A ranar Asabar kuwa za a yi wa shugaban ƙasa da sauran shugabanni kamar na addini gargajiya da gwamnonin jihohi har ma da sauran masu madafun iko kuma ana sa ran za a harka kai tsaye a kafafen yaɗa labarai na talabiji.
Shugaban hukumar lafiya matakin farko a Najeriya Dakta Fisal Shu’aib ya ce hukumomin da ke da alhaki a kan cutar Korona na daga sahun farko da za a fara yi wa rigakafin cutar.
A jiya Litinin hukumar lafiya matakin farko ta sanar da buɗe shafin intanet domin yin rijista ga waɗanda ke buƙatar rigakafin.
A Najeriya ana samun raguwar masu kamuwa da cutar kamar yadda ko da a jiya Litinin mutane 360 aka samu sun a ɗauke da cutar.