Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu siyar da kayayyaki daga Arewa zuwa kudancin Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga tsawon kwanaki.
Ƙugiyar ta janye yajin aikin ne bayan sun tattauna da gwamnatin tarayya ƙarƙashin gwamnan jihar Kogi.
Kamar yadda su ka bayyana, sun miƙa wasu buƙatu guda biyar bisa yarjejeniyar da suka yi.
Sannan ƙungiyar ta yi barazanar komawa yajin aikin matuƙar ba a biya buƙatun da aka musu ba.
Ƙungiyar ta shiga yajin aikin ne a sakamakon kashe mutanen Arewa mazauna kudu.
A sanadin yajin aikin da su ka shiga kayayyaki sun yi tsada sosai musamman kayan abinci.