Ƙungiyar Miyetti Allah ta goyi bayan harbe duk wanda aka samu da binda ƙirar AK-47.

Shugaban ƙungiyar Giɗaɗo Sidiƙƙi ne ya bayyana hakan a yau Alhamis cikin wata sanarwa da suka fitar bayan umarnin gwamnan jihar Anambra na harbe duk wanda aka samu da bindiga ƙirar AK-47.
Gwamnan jihar Anambara Wille Obiano ne ya bai wa jami’an tsaro umarnin harbe duk wanda aka samu da bindiga.

Hakan ya biyo bayan wani umarni daga fadar shugaban ƙasa wanda ta sanar da hakan ta bakin Mallam Garba Shehu.

Bayan zaman da shugaban ƙasa ya yi da shugabannin tsaro a Najeriya ranar Talata, an samar da wasu hanyoyi don ganin an kawo ƙarshen ƴan bindiga a ƙasar.
A cikin sanarwar da ƙungiyar Miyetti Allah ta fitar, ta bayyana goyon bayan ta a bisa matakin da aka ɗauka.