Gwamnatin jihar Zamfara ta saka dokar hana fita a garin Jangebe sakamakon rikicin da ya ɓarke yayin da aka mai da ƴan matan sakadiren da aka sace.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Sulaiman Anka ne ya bayyana hakan wanda y ace an rufe babbar kasuwar wadda ake zargi masu satar mutane na fakewa da ita wajen satar mutane.

A jiya Labara gwamnatin jihar ta miƙa ɗalibai mata waɗanda aka kuɓutar daga hannun masu satar mutane a jihar Zamfara.

A yayin da jami’an gwamnati da jami’an tsaro su ka shiga garin ne mutanen garin su ka fara jifan jami’an tsaro lamarin da ya yi sanadiyyar yin harbi sama.

A sakamakon hakan gwamnatin ta snya dokar hana fita tare da rufe babbar kasuwar garin.

Sai dai kwamishinan tsaro a jihar Abubakar Dauran y ace babu wata hayaniya da ta faru yayin da suka miƙa ɗaliban.

An sace ɗalibai mata ne a makon da ya gabata kuma gwamnatin da yi ƙoƙarin ceto su ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata bayan sulhu da aka yi tsakanin gwamnatin jihar da ƴan bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: