Mutane na ci gaba da tofa albarkacin bakin su a dagane da muƙabalar da gwamnatin jihar Kano ta shirya tsakanin Abduljabbar Sheik Nasir Kabara da malaman Kano.

A nashi ɓangaren mai alfarma sarkin musulmi Abubakar Sa’ad III yay i watsi da shirin da aka yi a kan muƙabalar.

Sarkin musulmi ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da Jama’atu Nasrul Islam ta fitar wadda yak e jagorantar.

A cikin sanarwar ƙungiyar ta ce babu bukatar zama da Malam bduljabbatr don yin muƙabala la’akari da kalaman sa.

Sarkijn muslmi ya ce a baya yay aba wa gwamnan jihar Kano a bisa dakatar da karatun malamin tare da rufe masallacin sa.

Kuma yana fata matsayar da ƙungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta ɗauka gwamnan zai yi amfani da ita wajen sauya matsayar da ya saka na yin muƙabalar da za a yi a ranar Lahadi mai zuwa.

Sarkin musulmi shi ne babban baƙo na musamman a yayin taron muƙabalar da aka shirya.

Shi ma a nasa ɓagaren Mallam Ibrahim Khalil y ace ba muƙabala ya dace a yi da Mallam Abduljabbar ba, illa tuhumar say a dace a yi.

Mallam Ibrahim Khalil shi ne shugaban majalisar malamai na jihohin arewa maso yamma kuma shugaban ta a jihar Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da karatun Shiek Abduljabbar ne a bisa zargin wasu kalamai da yake wanda gwamnatin ta ce sun a iya haddasa fitina.

A sakamakon hakan ta rufe masallacinsa tare da hana shi wa’azi, da kuma dakatar da saka karatun sa a kafafen yaɗa labarai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: