Rundunar sojin ƙasa a Najeriya ta bayyana ɓacewar wasu jami’an ta guda 101 bayan tagwayen hare-haren Boko harsam a garin Marte da kuma ƙaramar hukumar Dikwa a jihar Borno.

Daga cikin su akwai manyan soji guda 12 sai sauran sojojin guda 86 kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

A cikin wata sanarwa da dakarun sintiri na Operasion Lafiya Dole na jihar Borno su ka fitar sun ce sojojin ne sun ɓace ne yayin artabu tsakanin su da mayaƙan Boko Haram.

A kwanakin baya ne dai mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ta kwace garin marte kuma daga baya rundunar soji ta bayyana kwato garin  daga hannun su.

A makon da muke ciki kuwa mayaƙan Boko Haram sun sake kwace garin Dikwa duka a jihar Borno lamarin da har ta kai al’ummar garin su fice daga garin.

Daga baya ma dai rundunar sojin ta bayyana cewar ta sake kwato garin daga hannun mayaƙan Boko Haram.

a makon jiya ma dai sai da ƙungioyar ta harma wani makami cikin birnin Maiduguri lamarin da yay i sanadiyyar mutuwar wasu mutane da dama tare da jikkata wasu.

A jihar Borno ana fama da harin mayaƙan Boko Haram tsawon shekaru da dama yauin da sauran jihohin Aewa maso yamma ake fama da harin ƴan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: