Rundunar ƴan sanda a jihar Osun ta ce ta kuɓutar da wasu fasinjoji guda bakwai waɗanda aka yi garkuwa da su.

An sace fasinjojin ne a kan hanyar Osogbo zuwa Obokun a ranar Talata da daddare.

A yayin harin ƴan bindigan an kashe mutum guda tare da jikkata wasu mutane biyu

Sai dai ba a iya gano adadin mutanen da aka sace ba a hanyar amma guda bakwai daga ciki sun shaƙi iskar yanci.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Olawale Olokode ya ce jami’ansa da sauran jami’an tsaro ne suka shiga cikin dajin don ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace.

Kwamishinan ya bukaci al’ummar jihar da su bai wa ƴan sanda dukkan hadin kai ta hanyar bayanai don ganin an daƙile hare-hare a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: