Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya da su kawo ƙarshen ta’addanci kafin zuwan damina.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a jiya wajen maƙala anini ga sabbin hafsoshin tsaron.
Tun a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, majalisar dattijai a Najeriya ta tabbatar da su a matsayin sabbin hafsoshin tsaro bayan da shugaba Buhari ya naɗa su.

Shugaba Buhari ya ce al’ummar Najeriya na sa ido a kan ƙoƙarin da sabbin jami’an za su yi son kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya.

Sannan ya umarce su da su yi amfani da dukkan kwarewar aiki da ili wajen daƙile taɓarɓarewar tsaron da ake fuskanta a Najeriya.
Tun a watan Janairun shekarar 2021 shugaba Buhari ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron.
Kafin saka musu anini, yay i wani zaman sirri da su domin ganin an shawo kan barazanar tsaro da ake fuskanta.