Gwamnatin jihar Kwara ta rufe wasu makaranatu a jihar sakamakon rikici da ke faruwa sanadin Hijabi.

Aƙalla makarantu goma gwamnatin ta rufe sanadin hatsaniyar da ake fuskanta a kan saka hijabi a makarantar.

Sakatariya a ma’aikatar ilimi ta jihar Kemi Adeosun ce ta fitar da sanarwar hakan wadda ta ce makaranatun za su ci gaba da kasancewa a rufe kuma  ba a bayyana lokacin buɗewa ba.

A cewar sanarwar, gwamnatin ta duƙufa wajen yin adalci bisa kundin tsarin mulki na ƙasa da ya bai wa kowa haƙƙin sa.

Duk da cewar ƙungiyoyin addinin musulunci sun buƙaci a bai wa ƴaƴan su damar rufe ko da gashin kan su ne, amma mabiya kirista su ka ƙi aminta da buƙatar hakan.

Tun a baya makarantun sun kasance a rufe sai dai daga bisani gwamnatin ta buɗe su kuma aka ci gaba da samun hatsaniya a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: