Gwamnatin jihar Zamfara ta sassauta dokar hana fita a garin Jangebe garin da aka sace ɗalibai mata sama da 200 a baya.

Wani mazaunin garin mai suna Abubakar Zaki ne ya tabbatar da hakan wanda ya ce a yanzu haka sun koma harkokin su kamar kullum.

Gwamnatin jihar ce ta saka dokar hana fita a jihar bayan miƙa ɗaliban da ta kuɓutar zuwa ga iyayen su a garin.

Al’amarin da ya haifar da tarzoma kuma a dalilin hakan ne ya sa gwamnatin ta saka dokar hana fita tare da rufe babbar kasuwar garin.

Sai dai babu wani rahoto a kan buɗe kasuwar wadda gwamnatin ta ce ta na zargin ƴan bindiga na fakewa a cikin ta.

An sace ɗaliban mata ne sama da 300 a cewar rundunar ƴan sanda, sai dai gwamnatin ta ceto ɗalibai 279 wanda ta ce iya su kaɗai aka sace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: