Babbar kotun jihar wadda ke da zama a ƙaramar hukumar Ike Ekpene a jihar Akwa Ibom ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta samu matashin da laifin hallaka mahaifin sa da kan sa.
Matashin mai shekaru 31 a duniya ya hallaka mahaifin nasa a ranar 18 ga watan Nuwamban shekarar 2018 sannan ya binne shi a cikin banɗaki.
Yayin da yake karanto hukuncin, alƙalin kotun Augustine Odokwo y ace laifin ya saɓa da sashe na 326 (1) na cikin kundin dokar manyar laifuka na jihar na shekarar 2000.
A bisa dogaro da sashen da alƙalin ya bayyana, kotun ta yanke wa matashin hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Tun da farko ƴan sanda ne su ka gabatar da wanda ake zargi a gaban kotun bayan da aka same shi da aikata laifin.