Hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kama wasu mutane 57 waɗanda ta ke zargi sun a aikata damfara.

Hukumar EFCC reshen jihar Ibadan ce ta kama mutanen tare da kwato wasu makamai daga wasu dga cikin su.
Ana zargin mutanen ne da aikata damfara a yanar gizo, kuma hukumar ta kama su ne a otel daban-daban.

Sannan an kama motoci daga wajen su sai wayoyin hannu da n aura mai kwakwalwa wato kwamfuta ta tafi da gidan ka sai makamai guda biyu.

Shugaban sashen hulɗa da kafafen yaɗa labarai a hukumar Wilson Uwujaren ya ce da zarar sun kammala binmcike za su gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu domin su girbio abinda su ka shuga