Ƙungiyar lafiya ta duniya WHO ta ce babu wani dalilin dakatar da gudanar da allurar rigakafin cutar Korona ta Astra Zeneca.

Sakamakon ƙasashen da su ka dakatar da gudanar da rigakafin a kan al’ummar su, ƙungiyar ta ce kwamitin da ke lura da rigakafin ya bayar da rahon cewar babu alaƙa tsakanin rigakafin da cutar da ake zargi ta na haifar wa har ma ta hallaka mutane.
Mai Magana da yawun ƙungiyar Margaret Harris ce ta bayyana hakan a yayin taron manema labarai a Geneva.

Ta ce rigakafin ingantacciya ce kuma sun gamsu da ita a don haka su ke ƙara ƙarfin gwiwa ga ƙasashe da su ci gaba da amfani da ita.

An samar da rigakafin Astra Zeneca don rage yaɗuwar cutar Korona, yayin da wasu ƙasashen ke zargin rigakafin na da illar da har ta ke hallaka mutane.
A sakamakon hakan ne ma su ka dakatar da gudanar da ita.
Sai dai shirin Covax na taimaka wa ƙasashe masu rauni ta hanyar bas u rogakafin, ko da a Najeriya tuni aka shiga ƙaddamar da ita a kan al’ummar ƙasar har ma shugaban ya buƙaci al’ummar Najeriya da su fito domin a yi musu ita.