Wasu ƴan bindiga sun kai hari a kan wasu jami’an ƴan sanda da ke lura da shige da fice a kan babbar hanyar Buchi zuwa Jos.

A yayin harin an kashe wani jami’In ɗan sanda mai muƙamin isfeta.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Ahmed Wakili ne ya fitar da sanarwar ga ƴan jarida.

Ya ce an harbi jami’in nasu a yayin harin kuma sun yi ƙoƙarin kai shi asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Ɓalewa a nan aka tabbatar ya rasu.

Tuni aka girke jami’an tsaro masu yawa a yankin tare da gudanar da bincike mai zurfi a kan masu zirga-zirga don tabbatar da tsaro.

Kakakin ƴan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakili ya ce rundunar na takaicin mutuwar jami’in nasu tare da shan alwashin ci gaba da tabbatar da tsaro mai ɗorewa a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: