Shugaban rukunin gidajen gonar NANA Farms Nigeria Limited Alhaji Muhammadu Aminu Adamu y ace bay a goyon bayan yi wa ƴan bindiga afuwa kamar yadda wasu gwamnonin ke bayyana wa.

Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Abokin Tafiya da ake gabatarwa a Matashiya TV sau ɗaya a kowanne wata.
Ya ce babu dalilin da zai sa a yiwa ɗan bindiga afuwa kasancewar akwai n da ya addaba waɗanda ba su da haƙƙin komai a wuyan su.

Abba Boss ya ce muddin ana so a samu sauƙin ayyukan ƴan bindiga sai gwamnati ta tashi tsaye ta hanyar amfani da ƙarfin jami’an tsaro wajen murƙushe su.

Abba Boss ya ce haƙƙi ne a wuyan gwamnati ta tabbata ta bayar da tsaro ga al’ummar da ta ke shugaban ta.
Za mu kawo muku cikakken shirin a shafinmu na Youtube mai suna Mujallar Matashiya a gobe Talata.