Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi masu satar mutane da ke addabar makaranatu a jihohin ƙasar.

Muhammadu Buhari yay i wannan gargadi ne yayin da dake jawabin yaba wa dakarun soji waɗanda su ka kuɓutar da ɗalibai 180 daga cikin waɗanda aka sace a kwaleji da ke Kaduna.
A cikin sanarwar da ya fitar, mai Magana da yawun fadar shugaban ƙasa Mallam Garba Shehu ya yaba wa al’ummar gari waɗanda ke bayar da bayanann sirii ga jami’an tsaro.

Ko da a baya sai da shugaban ya bai wa ƴan bindiga wani wa’adi da su tuba su ajiye makaman su.

Kuma a cikin umarnin da shugaban ya bayar a baya-bayan nan akwai umrtar jami’an tsaro ha bindige uk wani da aka samu da bindiga ƙirar AK47 ba tare da izini ba.
A saƙon da Mallam Garba Shehu ya fitar kuwa ya ce Najeriya ba za ta lamunci ayyukan ƴan bindigan da su ke satar ɗalibai ba.
Muhammadu Buhari ya ce duk da cewar sojoji na iya samun kyan aikin yaƙar ƴan bindigan, amma ya zama wajibi al’umma su bayar da haɗin kai don maganace matsalar da ake fuekanta a kasar.