Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun sace ɗalibai guda biyu, waɗanda su ke karatu a wata jami’a a jihar Ogun.

Ƴan bindigan sun sace ɗalibai mata guda biyu a daren Lahadin da ta gabata wayewar jiya Litinin.
Rahotanni na nuni dacewar yan bindigan sun sace ɗaliban ne yayin da suke ƙoƙarin komawa masaukin su a daren Lahadin.

Mai Magana da yawun yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tuni dakarun su su ka duƙufa don ganin an ceto ɗaliban da aka sace.
Ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sandan jihar ne ya bayar da umarnin ceto ɗaliban, daga cikin tawagar jami’an akwai waɗanda ke aiki a sashen yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar yan sandna jihar.
Ya ce za su tabbata sun ceto ɗaliban ba tare da an cutar da ko guda daga cikin su ba.