Gwamnatin tarayyar Najeriya ta buƙaci iyaye da su ci gaba da kulawa da yaƴan su a makarantu.

Gwamnatin ta sake tabbatar da hakan ne a yayin zantawa da jaridar Punch.

Ƙaramin ministan ilimi a Najeriya Chukwumeka Nwajuba ya tabbatar da cewar gwamnatin ƙasar ba ta da damar kare dukkanin makaranatun ƙasar.

A cewar Chukwumeka sai iyaye sun ba da gudunmawar su wajen bai wa makarantu tsaro tare da kula da ƴaƴan su.

Sai dai gwamnatin ta bayar da dama ga kowanne makarantu da su kai rahoton duk wani abu da bas u gamsu da shi ba zuwa ga jami’an tsaro.

A cewar ministan mafi yawa daga cikin makarantun da ake da su a Najeriya tun daga na gwamnati har masu zaman kansu bas u da ingantaccen tsaro.

Ya ce makarantun a bude su ke da kowa zai iya shiga.

Wannan buƙata dai ta zo ne a yayin da aka tuntuɓi ɓangaren gwamnati a kan halin da ake ciki na satar ɗalibai da kuma matakin da gwamnatin ke shirin ɗauka.

Ko a baya sai da ministan tsaro a Najeriya ya buƙaci yan ƙasar da su dinga kare kan su a duk lokacin da aka kai musu hari.

A Najeriya ana ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan bindiga a sassa daban-daban musamman yankin Arewaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: