Babban hafsin sojin sama a Najeriya Air Marshal Isiyaka Amao ya ce a shirye su ke da su daƙile ayyukan ƴan bindiga a Najeriya.

Isiyaka Amo ya ce jami’an su a shirye suke domin yaƙar masu ayyukan ta’addanci a faɗin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci sansanin sojinn sama a jhar Kaduna.

Ya ce tuni shugaban ƙasa Muhammadu Buhari y aba su umarnin don yaƙar ayyukan ta’addanci a Najeriya don ganin mutane sun ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin kwanciyar hankali.

Daga cikin abin da su ka sa a gaba shi ne zaman lafiya tare da tabbatar da cewar manoma sun gudanar da noma a dukkanin fadin ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewar babban hafsin sojin saman ya ziyarci gwamnan  jihar Kaduna Mallam Nasir El’rufa’I a jiya Laraba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: