Rundunar ƴan sandan reshen babban birnin tarayyar Najriya Abuja sun kama mutane 10 waɗanda ake zargi da aikata fashi da makami.

Daga cikin mutanen akwai wasu da ak zargi da safarar miyagun kwayoyi zuwa garin.

An kama mutanen ne a yankin Mpape, Kado-biko, da kuma Life-Camp.

Mai Magana da yawun hukumar Maryam Yusuf ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce an kama mutanen ne a watan da muke ciki.

Baya ga mutanen da aka kama, an samu wasu makamai daga wajen su, sai kuma kayan maye da aka kwato daga wajen su.

Mafi yawa daga cikin mutanen da aka kama ƴan ƙasa da shekaru 30 ne.

Maryam yusuf ta ce za a gurfanar da mutanen da ake zargi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: