Minsitan tsaro a Najeriya Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya buƙaci al’ummar Najeriya fafren hula su taimaka wajen samar da tsaro a ƙasar.

Ministan ya ce Najeriya na cikin mawuyacin hali a sanadin ayyukan ƴan tada zaune tsaye.

Ministan ya bayyana haka ne a yau yayin wani taro da hukumar tsaro ta shiriya a babban birnin tarayya Abuja.

Bashir Magashi y ace har yanzu ana samun koma baya a kan al’amuran tsaro a Najeriya.

A cewar sa, duk da cewar a wasu lokutan ana samun nasara a fannin al’amuran tsaron, sai dai  hakan bay a hana nuni da koma bayan zaman lafiya a Najeriya.

Ya ce  ayyukan ƴan bindiga kamar fashi da makami, da garkuwa da mutane da kuma ayyukan wasu masu tada ƙayar baya a ƙasar na mayar da ita ta fuskar tsaro.

Bashir Magashi ya buƙaci al’ummar Najeriya fararen hula da su haɗa hannu da jami’an tsaro don cimma nasarar ayyukan samar da tsaro a Najeriya.

Ana ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a ɓangare daban-daban na Najeriya tun daga masu satar mutane fashi da makami da kuma ayyukan mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.

Leave a Reply

%d bloggers like this: