Gwamnan jihar Kano Dakta Absullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar za a samar da ƙofofin shiga kasuwaanni na zamani don ƙara inganta tsaro a jihar.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamna Kano Mallam Abba Anwar a fitar a yau.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wani taron kwanaki bakwai na musamman wanda aka shirya a Jigawa.
Ya ce ƙofofin da za a samar na zamani ne kuma su na ɗauke da na’urorin da za su bayyana duk wani mutum da yake ɗauke da makamai.

Ya ƙara da cewa yana da kyau kasuwanni a jihar su kasance cikin tsaro duk da cewar jihar Kano gari ne na zaman lafiya.
Taron da aka shirya an yi ne domin wayar da kan jama’a a kan muhimmancin yi wa filaye da gidaje rigista, sai kuma ƙoƙarin sauƙaƙa hanyar rigistar ga mabuƙata a cikin sauƙi.
An buɗe taron ne a jigawa.

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Talamiz wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Umar Namadi ya yaba wa jagororin jihohin a bisa zaman lafiya da ake a cikin su.

Taron ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar Kano, kwamishinoni da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: