Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta kama wani mutumi mai shekaru 70 a duniya wanda key i wa ƴan Boko Haram da masu garkuwa da mutane safarar kayan maye.

Mutumin mai suna Muhammed Rabi’u Wada ya shiga hannun hukumar ne a jihar Nijer yayin da dubun sa ta cika.
Mutumin ya kaance a ƙauyen dallawa na jihar Agadez a jamhuriyar Nijar, kuma an kama shi ne a Jebba ta jihar Neja.

Kwamadan hukumar NDLEA a jihar Neja ya tabbatar da cewar wanda aka kama sun sameshi da laifukan safarar kayan maye sai kuma taimaka wa wajen ruguza harkar tsaro a Najeriya.

Ana ci gaba da bincike a kan mutumin kuma da zarar sun kammala za su ɗauki mataki nag aba a bisa yadda doka ta yi tanadi.