Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram guda 48 tare da kuɓutar da wasu mutane daga hannun su.

Darantan yada labarai a hukumar na ƙasa Muhammad Yarima ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce jami’an sojin sun yi wa ƴan Boko Haram luguden wuta ne a yankin Chibok da Damboa kuma aka kashe mutane masu yawa tare da yi wa wasu raunin harbi.

An kuɓutar da wasu daga cikin mutane da mayaƙan su ka sace tare da kwace wata bindiga ƙirar AK47.

Daga cikin mutanen  da aka kuɓutar akwai wanda su ka samu raunin harbi a hannu da ƙafa.

Kakakin hukumar y ace an kai mutanen sahsen lura da lafiyar sojoji don kula da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: