Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Kojoli tare da sace mutane biyu .

Ƴan bindigan sun sace mutane ne bayan harbin bindiga sama a ƙauyen Kojoli da ke ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewar mutanen da aka sace jagorori ne a ƙauyen.

Sun kai harin ne a ranar Lahadi da daddare wayewar jiya KLitinin.

Ko a baya sai da ƴan bindigan su ka kai hari ƙauyen tare da sace shugan Fulani a yankin.

Karo na uku kenan da aka kai hari aka sace mutane a ƙauyen Kajoli na jihar Adamawa.

Maharani na shiga ƙauyen ne ɗauke da muggan makamai.

Harin ƴan bindiga dai ya karade jihohi mafi yawa a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: