Rundunar ƴan sandan jihar Ondo ta kama wata mai suna Blessing Jimoh wadda ake zargi ta kashe mahaifiyarta.

Matar mai shekaru 30 a duniya ta ce ta yi haka ne saboda umarnin da ta samu daga wani babban fasto din su.

Fastan ya bayyana mata cewar mahaifiyar tata it ace babbar matsalarta a rayuwa a don haka ya bata zaɓi ko ta kashe ta ko kuwa ta ci gaba da fuskantar matsaloli a cikin rayuwar ta.

Sai dai daga baya ta ce ta yi nadama a kan abinda ta aikata, a cewar ta ta yi ne domin samun sauƙin matsalolin da take fuskanta.

Ta yi amfani da adda ne wajen yanke kan mahaifiyar tata kuma daga baya dubunta ta cika.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Bolaji Salami ya ce sun samu bayanin haka ne daga ɗaya daga cikin ƴaƴan matar da aka kashe.

Sannan wadda ake zargi ta amsa laifinta kuma tuni aka miƙa ƙorafin zuwa babban sashen binciken masu aikata manyan laifuka don gudanar da bincike.

Kuma da zarar an kammala za a gurfanar da ita a gaban kotu domin yanke mata hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: