Wasu ƴan bindiga sun kashe shugabannin ƙungiyar Miyeti Allah a jihar Nassarawa.

An kashe Alhaji Muhammad Hussain a Garaku da ke ƙaramar hukumar Kokona a jihar.

A daren jiya wayewar yau Asabar ƴan bindigan su ka kashe mutanen biyu a kasuwar Garaku.

Mai magan da yawun yan sandan jihar ASP Rahman Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin kuma y ace tuni kwamishinan ƴan sandan jihar ya tura dakarun ƴan sandan na kan kace kwabo zuwa wajen.

Muhammad Umar kuwa da aka kashe shi ne shugaban ƙungiyr Miyetti Allah reshen ƙaramar hukumar Toto a jihar.

Rundunar ta ce ta tabbatar da mutuwar shugabannin biyu bayan da likitoci su ka basu rahoton cewa sun rasu.

Kuma za su ci gaba da bincike a kan lamarin don gano waɗanda su ka yi wannan aiki tare da ɗaukar matakin na shari’a a kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: