Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce za ta fara yin rijistar katin zaɓe daga ranatr 28 ga watan Yunin shekarar da muke ciki.

Za a yi katin zaɓen ne a dukkanin ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin Najeriya.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da su ka yi a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce za a shafe shekarar da muke ciki ana yin rigistar tare da ƙarin watanni uku na shekara mai kamawa.

Katin zaɓen na din-din-din za a yi wanda zai bayar da dama ga waɗanda su ka yi domin gudanar da zaɓen da ake tinkara a gaba.

Kuma y ace ba za a yi amfanin da katin shaidar zama ɗan ƙasa ba a yayin da ake karɓar bayanai daga waɗanda za a yi wa rijistar.

A kwanakin baya ma hukumar ta ayyana aniyar ƙarin mazaɓu a sassa daban-daban na ƙasar domin rage cunkoso a yayin gudanar da zaɓe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: