Aƙalla mabarata 250 ne su ka gudanar da zan ga-zanga sakamakon rashin basu sadaka da ake yi a jihar Oyo.

Biyo bayan zargin da ake yin a cewar, wasu daga cikin masu kudi na siyan kudin da ake bai wa mabaratan omin gudanar da wasu buƙatun nasu daban, a sakamakon hakan mutane a jihar su ka janye daga bai wa mabaratan sadaka.
Mabaratan sun gudanar da zanga-zangar ne a babban birnin jihar a ranar Alhamis.

A sakamakon zargin da ake yi musu na cewar masu kudi na siyan kudi a wajensu domin biyan buƙatarsu ta daban-, mabaratan sun musanta wannan zargi.

Sun nesanta kansu da hakan, sannan su k ace ƴan kasuwa da masu hayar babura na neman canji a wajensu ne domin samun ƙananan kudin da za su tafiyar da kasuwancin su.
Sun ce sun yi zanga-zangar ne domin nesanta kansu da wancan zargi saboda kada a hukunta su da laifin da ba sa aikatawa.
Mafi yawa daga cikin mabaratan da su ka yi zanga-zangar makafi ne.