Ƙasar saudiyya na duba yuwuwar ƙara adadin mutanen da za su yi umara a azumin bana.

Mataimakin ministan kula da aikin hajji a ƙasar Abdulfatah Mashat ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da gidan talabiji na Al’arabiyya.
Ya ce za a yi wa dukkanin masu kula da masallacin ka’abah rigakafin cutar Korona.

Gudanar da rigakafin zai bayar da dama ga musulmi masu yawa don ganin sun gudanar da Umara a azumin bana.

Sannan za a tabbatar kwamitocin da aka kafa don kula da matakan kariya a kan cutar za su tabbatar dukkaninsu sun yi aikin su yadda ya kamata musamman a masallacin Makkah da na Madina.
Tun da farko an rage yawan masu zuwa Umara a ƙasashen duniya sakamakon ɓullar cutar Korona.
Sai dai daga baya an samar da rigakafin cutar wanda ake sa ran musulmi da yawa za su samu damar gudanar da Umrah da aikin hajji a bana.