Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El’rufa’I ya ce gwamnatin jihar za ta hukunta duk wanda ta samu na tattauna wa da ƴan bidniga a jihar.

Haka kuma za ta hukunta dun wanda ya bayar da kuɗin fansa ga ƴan bindiga ko masu garkuwa da mutane a madadin ta.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro a jihar ya fitar, ya musanta zargin da ake na cewar gwamnatin ta kafa wani kwamiti da zai tattauna da ƴan bindigan.

Sanarwar ta ce babu wani kwamiti da aka kafa sannan babu tsarin kafa kwamitin domin tattauna wa da ƴan bindiga.

Gwamnatin ta sake jaddada cewar ba za ta tattauna da yan bindiga don yin sulhu a bisa hare-haren da su ke kai w aba.

Sannan sun buƙaci a kai rahoton duk wani da aka samu ya na tattauna wa ko biyan kuɗin fansa a madadin gwamnatin.

Tun a baya ma dai gwamnan jihar ya bayyana cewar ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba a sakamakon haka ma ya sa su ke tattauna wa da gwamnan jihar Neja domin shawo kan matsalar tsaro a tsakanin jihohin biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: