Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wasu ƴan bindiga sun kai hari garin har su ka kashe mutane takwas.

An kai harin ne a Kajuru na ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro a jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.

Ƴan bindigan sun fara buɗe wuta a kan wata motar ƙirar bas da wata akori kura wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutane biyar nan takje sai wasu da su ka jikkata.

Haka kuma ƴan bindigan sun kuma tare babbar hanyar fita daga ƙauyen Doka kuma su ka buɗe wa wata babbar mota wuta lamarin da ya  yi sanadiyyar mutuwar direban.

Sai ƙauyen Inlowo da ƴan bindiga su ka kashe mutum guda tare da sace shanu 180.

Haka kuma ƴan bindigan sun buɗe wuta a kan wata ƙaramar mota wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutum guda da jikkata wasu a ciki.

Sanarwar ta fita ne kwana guda da bayyana cewar gwamnatin jihar Kaduna ta ceto ɗalibai biyar daga cikin waɗanda aka sace a wata kwaleji a kwanakin baya.An Kashe Mutane Takwas A Kaduna

Leave a Reply

%d bloggers like this: