Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun sace mutane goma tare da kashe mutum guda a garin Gurmana na ƙaramar hukumar shiroro a jihar Neja.
Ƴan bindigan sun shiga garin ne a kan babura sannan su ka fara harbi kan mai uwa da wabi.
Daga bisani kuma su ka fara shiga gida ɗaya bayan ɗaya sun a kwashe kayan mutane, sannan su ka ƙone kayan abincin mutanen garin.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a daren jiya wayewar yau Asabar, sannan su ka ƙone gidaje a garin kuma su ka yi awon gaba da mutane goma.
Yayin tuntuɓar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar bai sami damar ɗaga way aba har ;lokacin da muke kawo muku wannan labara.
Sai dai kakakin haɗaɗɗiyar ƙungiyar Shiroro Kwamared Salisu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin kamar yadda ya bayyana wa jaridar Punch.