Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki aniyar aurar da mata masu zaman kansu a jihar a wani salon a kawo ƙarshen ɗabi’ar karuwnci a jihar..
Sannan gwamnatin za ta mayar da mata masu zaman kansu waɗanda ba ƴan jihar ba zuwa jihohin su.
Kwamishinan da ke kula da hukumar hizbah a jihar Brista Aminu Balarabe ne ya bayyana hakan a yayin gudanarv da taron wayar da kai a sakamakon watan azumi na bana.
A cikin tsarin da za a yi za su tabbatar an sauya rayuwar matan ta yadda za su yi rayuwa mai inganci.
A binciken da su ka gudanar sun gano cewa, mafi yawa daga cikin matan na faɗa wa ɗabi’atr ne a sakamakon tsangwama ko talaci.
Kuma za a tabbatar an samawa matan sana’o’in da za su dogara da kansu domin kyautata rayuwar su.
Za su yi aikinne ne da timakon hukumar hizbah ta jihar wadda ita za ta tsara yadda za a gudanar da auran.
Sannan gwamnatin jihar za ta tabbatar ta haɗa kai da gwamnatocin ƙananan hukumomi don ganin an kawo ƙarshen ɗabi’ar baki ɗaya.