Gwamnatin jihar Kaduna ta gudanar da taro da malaman addinin musulunci a jihar a domin samar da daidaito wajen wa’azin da zai haifar da rarrabuwar kai.

Darakta mai kula da harkokin addinin musulunci a jihar Kaduna Sheik Jamil ALbani Zaria ya bayyana cewar, gwamnatin ta ga dacewar haɗa taron ne domin samar da matsaya a tsakanin malaman.
Ya ƙara da cewa gwamnatin na buƙatar samar da fahimta a tsakanin kowanne ɓangare domin kaucewa gabatar da wa’azin da zai haifar da rarrabuwar kai ga musulmi.

Sheik Ishaƙ Almadani ya bayyana dalilai da ke sanya malamai su yi amfani da mumbarin wa’azi wajen jefa aƙidar su, wanda y ace hakan ya samo asali ne daga ƙin yin abu domin Allah.

Babban limamin masallacin Sheik Ɗahiru Bauchi Sheik Hashim Bindawa wanda ya sake tabbatar da cewar da malamai za su gaskata abinda Allah ya faɗa da ba za a samu wasu da za su dinga faɗar abinda su ka ga dam aba.
A yayin taron an tattauna muhimman batutuwa tare da samar da hanyar kaucewa yaɗuwar cutar Korona musamman a wannan lokaci da ake gabatar da wa’azi.