Gwamnatin jihar Katsina ta amince da saka karnuna a makarantun kwana na jihar a wani salon a daƙile satar ɗalibai a jihar.
Kwamishinan ilimi a jihar Badamasi Charanci ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce za a yi amfani da karnukan ne domin taimawa wajen samar da tsaro a makarantun kwana na jihar.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta amince da saka karnukan ne ganin yadda su ke saurin gano masu laifi fiye da mutane.
Sannan karnukan za su dinga sanar da ɗalibai da jami’an tsaro yayin da wasu ƴan bindiga su ka yi ƙoƙarin kai hari makaranatun.
Shawara ce dai wadda aka samu daga ɓagaren tsaro a jihar har ma su ka bayar da misalin yadfda ake amfani da karnukan a ɗaiɗaikun gidaje domin samar da tsaro.
Gwamnan jihar Aminu Bello Masari y ace an sake duba hanoyin tabbatar da tsaro a makarantun kwana kafin bude su.
A baya bayanan nan wasu ƴan bindiga su ka sace wasu ɗalibai a makarantar kwana ta ƙanƙara a jihar Katsina.