Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari helkwatar ƴan sanda shiyya ta 13 a jihar Anambara.

A yayin harin da su ka kai an kashe ƴan sanda biyu tare da ƙone baben hawa a ciki.

Rahotanni daga jihar na nuni da cewar mutane na cikin fargaba a sakamakon harin da aka kai helkwatar ƴan sadan.

Ko a daren Lahadi sai da aka kashe wasu mutane uku a ƙaramar hukumar Awka south ta jihar Anambara.

Sai dai ba a tantance mutanen da su ka jikkata ba a yayin da aka kai harin.

a wani yanki na kudancin Najeriya ana zargin masu fafutukar kafa ƙasar BIAFRA da kitsa hare-hare kamar yadda rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi zargi.

Sai dai ba a bayyana wadanda ake zargi da kai harin jihr Anambara ba.

Wani jami’I ya bayyana cewar ƴan sandan sun yi ƙoƙarin hana ƴan bindigan shiga wjen adana makaman ƴan sanda da ke sansanin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: