Majalisar dattijhai a Najeriya ta buƙaci gwamnonin jihohi da su bai wa ma’aikatar shari’a damar cin gashin kan ta.

Shugaban kwamitin ɓangaren shari’a da ƴancin Ɗan’’adam Opeyemi Bamidele ne ya bayyana wa manema labarai hakan.
Ya ce akwai buƙatar a bai wa ɓangaren shari’a damar cin gashin kansa domin tabbatar da damokaradiyya a Najeriya.

A cewar shugaban kwamitin, hakan ba zai rage wa komai komai ba.

Ya ƙara da cewa ƴancin ɓangaresn shari’a a abu ne da ake buƙatar sasantawa ba illa bashi dama kai tsaye.
Ƙungiyar ma’aikatan sharia a Najeriya ta tsunduma yajin aiki ne bayan gwamnonin jihohi sun ƙi aminta da baiwa ɓangaren damar cin gashin kan sa.