Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da tsarin ƙungiyar gwamnoni a kan tsarin bai wa ma’aikatan shari’a damar cin gashin kan su.
A sakamakon yajin aikin da ma’aikatan shari’a ke ci gaba da yi a Najeriya na ganin an ba su damar cin gashin kan su daga gwamnonin jihohi.
Ƙungiyar lauyoyi ta ziyarci gwamna Ganduje tare da miƙa masa wasiƙa daga uwar ƙungiyar ta ƙasa.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa laban gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar a yau, sanarwar ta ce gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin da ƙungiyar lauyoyi su ka ziyarceshi yau a ofishin sa.
Ganduje ya ce gwamnatin sa ta gudanar tsari mai kyau a ɓangaren shari’a sannan zai ci gaba da bai wa bangaren gudunmawa don ganin ya samu tagomashi mai yawa.
Daga cikin ayyukan da gwamnan ya lissafa har da samar da babban kotun ɗaukaka ƙara wadda ta lashe maƙudan kuɗaɗe masu tarin yawa
Ganduje ya amince da tsarin bai wa ɓangaren shari’a damar cin gashin kan ta kuma a shirye yake da yay i aiki da hakan.
A nasa ɓangaren shugaban ƙungiyar lauyoyi a jihar Kano Barista Aminu Sani Gadanya ya yabawa gwamna Ganduje a bisa alƙawarin da yayi tare da jinjina masa ganin yadda yak e bai wa bangaren muhimmanci a gwamnatin sa.