Aƙalla mutane 18 wasu ƴan bindiga su ka sace a cikin wata motar haya yayin da su ke tafiya a jihar Oyo.
Matafiyan da su ka nufi jihar Oyo bayan sun taho daga Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Al’amarin ya faru a safiyar yau Alhamis bayan ƴan bindigan sun tare babbar hanyar tare da tilastawa matafiyan tsayawa sannan su ka tafi da su.
Wasu mazauna Igboora da Eruwa sun bayyana cewar, masu garkuwa da mutanen su kan tare hanyar ne a kullum.
Sannan sun yi ƙoƙarin sanar da hukumar ƴan sanda da wasu daga cikin jagororin su a matakin shugabanci amma abin ya ci tura.
Mun yi ƙoƙarin tuntubar kakakin hukumar ƴan sanda domin tabbatar da faruwar lamarin, sai dai har lokacin da muka kammala haɗa labarin ba mu ji daga gareshi ba.