Rahotanni daga jihar Kaduna na tabbatar da cewar a daren jiya Laraba wayewar yau Alhamis wasu yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan lafiya biyu a babban asibitin jihar.

Ƴan bindiga sun kutsa cikin babban asibitin ne da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar Kajuru Cafra Casino yay i kira ga al’ummar sa da su kwantar da hankalin su domin sun a ƙoƙari don gudanar da bincike a kai.

Wani likiti a  asibitin ya shaida cewar ƴan bindigan na ɗauke da muggan makamai yayin da su ka shiga asibitin.

Mutane biyun da aka sace an ce likitoci ne.

Awanni kaɗan da ƴan bindiga su ka sace wasu ɗalibai da ke makaranatar Greenfield a jihar.

Sai dai har zuwa lokacin da mu ke kammala wannan labarin hukumomi a jihar bas u magantu a kan lamarin ba.

Jihar Kaduna ta yi ƙaurin suna cikin jihohin da ake fuskantar ayyukan masu garkuwa da mutane, fashi da makami da satar shanu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: