Gwamnatin jihar Kano ta aike da saƙon ta’aziyya a madadin gwamnatin da al’ummar Kano baki ɗaya.

A cikin sanarwar da kwamishinan yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Muhammad Garba ya fitar, gwamnatin ta bayyana rashin mai babban daki a matsayin babban rashi da aka yi duba ga irin kyawawan halayen ta

Masarautar Kano ta tabbatar da rasuwar hajiya Maryam do Bayero matar tsohon sarkin Kano marigari Dakta Ado Bayero.

Hajiya Maryam mahaifiya ce ga sarkin Kano na yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.

Ta rasu ta na da shekaru 80 a duniya a ƙasar Masar bayan gajeruwar rashin lafiya.

A yau Asabar ta rasu da misalign ƙarfe tara na safe.

A na sa ran za a yi jana’izar ta gobe Lahadi bayan an kawo gawar ta daga ƙasar Masar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: