Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin za ta yi amfani da duk ƙarfin ta domin magance ayyukan fashi da kuma satar mutane da ake yi a ƙasar.

Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan ɗaliban da aka sace a jihar Kaduna.
a cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun fadar gwamnatin tarayya Mallam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban ƙasar na jimamin rashi da aka yin a ɗaliban.

Sannan y ace abin baƙin ciki ne ganin yadda wasu ƴan siyasa ke ƙara rura wutar abin da ke faruwa.

Muhammadu Buhari ya buƙaci hadin kan al’umma domin magance matsalar da ake fuskanta ta rashin tsaro a ƙasar.

Muhammadu Buhari ya kira ta’addancin da ke faruwa da munanan hare-hare garin yadda ya k faruwa a kai a kai.

Gwamnatin jihar Kaduna ce ta tabbatar da kisan mutane uku ɗalibai a makarantar Greenfield waɗanda ƴan bindiga su ka sace a makon da muke ciki.

Kwamishinan tsaro a jihar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce an ga gawar ɗalibai guda uku a ƙauyen kwanar Bature kusa da makaranatar da aka sace su.

A ranar Talata ƴan bindigan su ka sace daliban wadanda har yanzu ba a kai ga gano adadin sub a.

Kafin sace ɗaliban na ranar Talata, a baya an sace wasu ɗaliban kwaleji a Kaduna kuma har yanzu akwai sauran ɗalibai 29 a hannun ƴan bindigan.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewar ba za ta yi sulhu da ƴan bindiga ba, haka kuma za ta hukunta duk wanda ya je yin sulhu da su ko biyan kudin fansa a madadin ta.

Jihar Kaduna na fuskantar hare-haren yan bindiga, masu garkuwa da mutane har ma da fashi da makami.

Leave a Reply

%d bloggers like this: