Rundunar ƴan sanda a Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani baturen ƴan sanda wato DPO tare da yaransa takwas a jihar Kebbi.

A sakamakon haka mazauna ƙauyen Makuku sun fara tserewa a sakamakon abin da ya faru.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar ASP Nafi’u Abubakar ne ya shaida hakan wanda ya ce lamarin ya faru ne a jiya Lahadi.

Jami’in da yaran sa sun mutu ne yayin da su ka kai ɗauki ƙauyen Makuku bayan ya samu labarin ƴan bindiga sun kai hari a kan mazauna ƙauyen.

Rahotanni na nuni da cewar an buƙaci agajin hukumar soji kuma nan da nan su ka kai ɗauki a garin.

Sai dai muutanen yankunan na tserewa domin tsira da rayuwar su.

Ko a makon da ya gabata ma sai da aka kai hari wasu ƙauyuka a jihar tare da sace shanu masu yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: