A Geidam ta jihar Yobe kuwa mazauna garin na ci gaba da gudun hijira a sakamakon ci gaba da kai hare-hare gain wanda ƙungiyar Boko Haram ke kai wa.

Tun a ranar Juma’a mayaƙan su ka ci gaba da kai hare-haren tare da ƙone gidaje da kuma tafiya da kayyakin abinci na jama’a.
An ci gaba da fafatawa tsakanin mayaƙan da rundunar soji wanda tuni aka aike da su garin.
tun da farko mayaƙan sun shiga garin tare da raba wata takarda wadda ke nuni da buƙatar hadin kan mutanen don mara musu baya tare da ƙoƙarin kafa tutar su a garin.

Da farko sai da mayaƙan su ka tsagaita wuta bayan da ake aike da jirgin soji kuma daga bisani su ka farwa mutanen garin.

A ƴan kanakin nan mayaƙan Boko Haram na ƙaddamar da hare-hare a jihohin gabashin Najeriya, jihohin da su ka shafe sama da shekaru 10 su na fuskantar rikicin Boko Haram.