Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya na nuni da cewar mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kwaci wasu ƙauyuka tare da kafa tutar su a ciki.

Ƙauyukan na ƙarƙashin ƙanan hukumomi biyu na jihar Shiroro da Kaure.
Gwamnan jihar ya tabbatar da cewar mayaƙan Boko Haram sun kafa tutar su a garin.

Gwamnatin ta ce mayaƙan na son yin amfani da yankin ne kamar yadda su ka mamaye dajin sambisa.

An tsaurara matakan tsaro a sakamakon hakan kamar yadda babban mai ba gwamna shawara a kan watsa labarai ya bayyana.
Tun a baya sai da gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar mayaƙan na shirin kafa sansani a jihar.