Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari sansanin ƴan gudun hijira a jihar Benue.

Maharan sun kai harin tare da kashe mutane ƴan gudun hijira bakwai a sansanin nasu da ke Abagena a ƙaramar hukumar Makurdi babban birnin jihar.
Ƴan bindigan sun shiga sansanin a daren Talata tare da harbi kan mai uwa da wabi.

Baya ga mutane bakwai da su ka mutu akwai wasu da yawa waɗanda su ka samu rauni a sakamakon harin.

Tuni aka miƙa gawarwakin zuwa asibitin koyarwa na jihar su kuwa waɗanda su ka samu rauni su ke karɓar kulawa daga ma’aikatan lafiya.
Gwamnan jihar wanda ya kai ziyara sansanin a jiya ya buƙaci shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya bai wa al’amuran tsaro muhimmanci don kare rayukan al’ummar ƙasar.