Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar uku ga watan Mayu mai kamawa a matsayin ranar hutu domin girmama ma’aikata ta duniya.
Ministan cikin gida Mista Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatiun tarayya, yana mai taya ma’aikata murnar ranar su a duniya.
Ranar ma’aikatan zai kasance ranar Litinin mai zuwa, sanna ma’aikata za su kasance a gida don girmama ranar ta su.
Ministan ya godewa ma’aikatan a bisa mutunta tsrae-tsaren gwamnati da suke yi domin ci gaban ƙasa.
Majalisar ɗinkin duniya ce dai ta ware ranar ɗaya ga watan mayun kowacce shekara a matsayin ranar ma’aikata ta duniya.